A yau Asabar wakilan Amurka da na kungiyar Taliban da ke Afghanistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Doha, babban birnin Qatar.
Yarjejeniyar na zuwa ne bayan da aka kwashe kusan shekara 19 ana yaki a kasar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, na daga cikin wadanda suka shaida wannan matsaya da ake kokarin cimma, wacce ake sa ran za ta zama sharar fage ga yunkurin kawo karshen wannan yaki.
Ana fatan za kuma ta ba da damar rage yawan dakarun Amurka a kasar ta Afghanistan daga 13,000 zuwa 8,600.
Gabanin hakan, tsohon Shugaba Afghanistan Hamid Karzhai ya fadawa Muryar Amurka cewa, “suna masu matukar farin ciki da wannan yarjejeniya da aka kulla.”