A lokacin wani taron manema labarai na hadin guywa da firayin ministan kasar Italiya, Giuseppe Conte, wani dan jarida ya tambayi Trump ko zai iya ganawa da shugaban Iran Hassan Rouhani?
“Na yarda da zaman tattaunawa,” amsar da Trump ya maida kenan. Ya cigaba da cewa, “yin magana da mutane, musamman idan akan batutuwan da za iya kawar da yaki, mace-mace, yunwa da kuma sauran wasu abubuwa ne, ai sai a gana. Babu wani aibi a zaman tattaunawa.
Trump ya ambaci tattaunawar ido-da-ido da yayi kwanan nan da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un da na Rasha Vladimir Putin a matsayin misalin matakin diplomasiyyar kai tsaye da ya dauka akan shugabannin da aka dauka a matsayin masu adawa da muradan Amurka.
Da aka tambaye shi ko yana da wasu bukatu da zai nema daga Iran kafin tattaunawar, sai ya ce babu wasu ka’idoddi Idan Iran tana so a tattauna, zan tattauna.