Amurka Ta Zargi Iran Da Ruruta Rikicin Yemen Ta Wajen Taimaka Ma 'Yan Tawaye

  • Ibrahim Garba

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Nikki Haley

Yayin da rikicin kasar Yamal (Yemen) ke kara kazancewa tun bayan kisan tsohon Shugaban kasar Ali Abdullah Saleh, Amurka ta zargi kasar Iran da taimaka ma 'yan tawayen Houthi da manyan makamai a wannan yakin da ake ganin rigima ce ta tsakanin Saudiyya da Iran din a fakaice.

Wata babbar jami’ar gwamnatin Amurka ta fadi jiya Alhamis cewa Amurka na da “tabbatacciyar shaidar” cewa Iran na samar da makamai ga ‘yan tawaye a Yamal, abin da ya saba ka’ida; kuma hakan wani bangare ne na halayya marasa kyau da ta ke nunawa a yankin.

“A cikin wannan gidan ajiye kayan akwai cikakkiyar shaidar cewa Iran na ta tara makamai ba bisa ka’ida ba; wadanda ta kan samo bayan ta kai hari kai tsaye kan aminanmu da ke yankin,” abin da Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta gaya ma wani taron ‘yan jarida a wani sansanin sojan Amurka Kenan a birnin Washington DC.

Haley ta yi wannan bayanin ne yayin da ta ke tsaye gaban wani tarin baraguzai, da ta ce an kwaso ne daga wani wurin da ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran a Yamal su ka harba makami mai linzami mai gajeran zango zuwa cikin kasar Saudiyya da ya dira kan wani filin jirgin saman farar hula. Ta ce Amurka za ta gayyaci mambobin MDD da kuma mambobin kwamitin sulhun MDD su yi nazarin baraguzan.

Nan da nan bayan taron manema labaran da Haley ta kira kasar Iran ta fitar da takardar martani, inda ta yi watsi da zarge-zargen da cewa marasa tushe ne, kuma na marasa hankali, masu neman tayar da fitina kuma mai cike da hadari.”