Babban jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka -FBI- James Comey yace kasar China ce kan gaba a jerin kasashen duniya dake satar shiga yanar gizo na masana’antun Amurka, abinda yake janyowa Amurka asarar biliyoyin daloli.
Comey ya shaidawa shirin tashar talabijin na CBS 60 minutes jiya Lahadi cewa, ba da wasa China take yi ba a kokarinta na satar sirrin da zai amfani harkokin kasuwanci da masana’antunta.
Yace ba ya yiwuwa a iya lissafta asarar da kamfanonin Amurka ke yi, sai dai yace zai kai biliyoyin daloli.
Satar dabaru da kuma sirrin kamfanonin Amurka da China ko kuma wadansu ke yi, zai iya janyo asarar guraban ayyuka da dama, da kuma kudin shiga.
Bisa ga cewar Comey, satar shiga shafin yanar gizo na kamfanonin da barayin yanar gizo da kuma ‘yan ta’addar internet ke yi, ya yi yawa ainun, kuma Amurkawa basu dauki hadarin wannan irin satar da muhimmanci yadda ya kamata ba.
Amurka tana tuhumar wadansu ‘yan kasar China biyar kwararru a fannin aikin soja da satar bayanan internet a watan Mayu, abinda ya tada hankalin China, wadda ta musanta cewa tana satar shiga yanar gizon Amurka ta kuma zargi Amurka da leken sirrin masana’antunta.