Yadda Amurka Ta Zarce Kowace Kasa a Duniya a Yawan Masu Coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump

Yayin da Amurka ta dara China da sauran kasashen duniya a yawan wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Coronavirus, rahotanni na nuni da cewa, Shugaba Donald Trump bai nuna alamar damuwa ba kan yadda annobar ke ci gaba da yin ta’adi a kasar ba.

Yayin wani taron manema labarai da kwamitin da aka kafa domin yaki da cutar ta COVID-19 a Amurka ya jagoranta a jiya Alhamis a Fadar White House, shugaba Trump ya gayyawa Amurkawa da su “kwantar da hankulansu, su zauna a gida, yana mai cewa, “ana samun ci gaba.”

Ya kuma kara da cewa, a mako mai zuwa hukumomin Amurka za su fitar da wata sanarwa kan yadda za a sassauta umurnin ba da tazara da sauran matakan da gwamnatin ta dauka, inda ya kuma ya ba da shawarar cewa, mai yiwuwa a dawo da harkokin kasuwanci a sassan kasar da cutar ta Coronavirus ba ta yi kamari ba.

Sai dai kwararru a fannin lafiya sun yi gargadin cewa, har yanzu akwai yankunan kasar da ba su fuskanci ainihin radadin cutar ba.

A halin da ake ciki an tabbatar da mutum dubu 82 na dauke da cutar ta COVID-19 a Amurka, sannan kusan 1,200 sun riga mu gidan gaskiya.