Amurka Ta Zabi Mai Kula Da Lamarin Coronavirus A Kasar

A jiya Alhamis ne mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya nada Debbie Birx masaniyar harkar kiwon lafiya na kasa da kasa ta zama jami’ar kula da lamura da suka shafi coronavirus a fadar White House, lamarin da zai wayar da gwamnatin a kan yunkurinta na yaki da yaduwar cutar a cikin kasar.

Birx likita ce kuma a matsayinta na babbar jakada a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, yanzu ita ce ke jagorntar yunkurin gwamnati na yaki da cutar kanjamau a duniya.

Zata rika bada rahoto ga Pence, wanda shugaba Donald Trump ya nada a ranar Laraba ya kula da martanin gwamnatin Amurka game da babbar kalubalen kiwon lafiya da ya addabi duniya kana zata karu cikin rukunin yaki da coronavirus karkashin jagorancin sakataren kiwon lafiya da ayyukan jama’a Alex Azar. Birx ma’aikaiyar gwamnati ce da tsohon shugaban kasa Barack Obama ya bata aikin kula da cutar kanjamau.