Amurka Ta Yi Wa China Kashedi Kan Mamayar Da Ta Ke Yi

Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper a Jamus, ranar 15 ga watan Fabrariru 2020.

A yau Asabar, Sakataren tsaron Amurka, Mark Esper, ya yi kira ga shugabannin duniya, da su “farga” domin kalubalantar yadda China ke kokarin mamaye al’amuran duniya.

Esper na magana ne yayin taron kasashen da ake yi kan matsalolin da ke addabar duniya a Munich.

Ya kuma kara da cewa Chinan, wacce ta fi kowace kasa yawan jama’a a duniya, na kokarin ta ga ta cimma burinta ta kowanne hali.

Esper ya kuma jaddada matsayar cewa, ba wai Amurka na takalar China da fada ba ne, amma ya yi nuni da cewa, Chinan na kokarin ta ga ta fadada karfin sojinta nan da zuwa shekarar 2035 ta kuma mamaye dakarun yankin Asiya nan da shekarar 2049.

Ya kuma zargi Chinan da yin katsalandan a harkokin nahiyar turai da sauran wurare da ke wajen kasarta.

"Ya zama dole gwamnatin China ta sauya manufofinta da irin halayenta, idan kuma ba haka ba, ba mu da zabin da ya fi mana mu kare tsare-tsarenmu.” Inji Esper.

Sai dai Ministan harkokin wajen Chinan, Wang Yi, ya ce zarge-zargen na Amurka ba su da tushe ballantana makama.