Amurka Ta Yi Alkawarin Saidawa Sojojin Indiya Makamai

Shugaban Amurka Donald Trump da Firayim Minista Narendra Modi na Indiya

A Yau Litinin, Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta sanya hannu kan yarjejeniyar sayar da makamai ga sojojin India, da suka hada da jirage masu saukar ungulu da sauransu.

An yi kiyasin kudaden makaman zasu kai dala biliyan uku.

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne yayin da aka tarbe shi a birnin Ahmedabad, inda tarin mutane sama da 100,000 suka hallara don su saurari jawabinsa da na Firayim Minista Narendra Modi na Indiya.

Kafin ziyarar, Trump ya ce sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba zata kasance cikin dalilin wannan tafiya ba.

Amma a cikin jawabin nasa, ya yi alkawarin kasashen biyu za su kulla "daya daga cikin manyan yarjeniyoyin kasuwanci mafi muhimmanci," ya kuma ce yana sa ran shi da Modi za su iya " cimma kyakkyawar yarjejeniya da zata amfani kasashen biyu