Amurka Ta Umarci Dukkan Ma'aikatanta Wadanda Aikinsu Ba Na Musamman Ba Su Bar Mogadishu.

Wani hafsan mayakan Turkiyya yake raka shugaban Somalia a bikin kaddamar da sansanin sojinta a Somalia.

Wannan matakin ya biyo barazana da ake shirin aunawa kan ma'aikatan.

Amurka ta umarci dukkan ma'aikatan ofishin jakadancin ta a Somalia wadanda ayyukansa ba su da muhimanci ainun, su bar Mogadishu babban birnin kasar, saboda "bayanai na barazana akan su."

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar yau Asabar, tana da nasaba ga tashar jirgin saman kasar, wacce rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar hada kan kasashen Afirka ke baiwa kariyaka, kashin ikon wani kamfanin kasar Turkiyya.

"Saboda barazana kai tsaye kan wasu ma'aikatan Amurka a tashar saukar jirgin sama a Mogadishu, ofishin jakadancin ya umarci ma'aikatan sa wadand aikinsu ba wajibi bane su bar Mogadishu, har sai abunda hali yayi," kamar yadda sanarwar ta fada.

Haka nan sanarwar ta umarci Amurkawa wadanda suka yanke shawarar za su ci gaba da zama a kasar to su yi taka-tsantsan.