Amurka Ta Umarci Amurkawan dake Kasar Burundi Su Fice

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Biyo bayan rikicin da ya barke a Burundi da ya haddasa rasa rayuka fiye da tamanin, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci amurkawa dake zaune a kasar Burundin da su fice

Gwamnatin Amurka, ta umarci duk ‘yan kasar da ke zaune a Burundi da su fice daga kasar, bayan mummunan fadan da ya barke a makon da ya gabata da ya hada da sojoji da ‘yan sanda.

A jiya Lahadin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce ta ba da umarnin a kwashe wasu daga cikin ma’aikatanta tare da iyalansu, yayin da rikicin siyasar kasar ta Burundi ke kara ta’azzara bayan zabukan da aka yi da yunkurin juyin mulki a watan Mayun da ya gabata.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Amurka, ta kuma yi gargadin cewa ofishin jakadancin Amurkan, zai iya ba da takaitaccen taimako ne kawai a kasar ta Burundi ga Amurkawa.

Akalla mutane 80 aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata a Bujumbura, babban birnin kasar, bayan da wasu mahara suka kai samame a wani sansanin soji, inda aka samu hasarar rayuka, ciki har da jami’an tsaro takwas da kuma wasu daga cikin maharan da dama, kamar yadda wani kakakin soji ya bayyana.