Amurka Ta Tallafawa Nijer Da Rikakafin Johnson & Johnson 15200

za2

za2

Hukumomin jamhuriyar Nijer sun karbi wani ruunin tallafin allurar riga kafin covid 19 samfarin Johnson & Johnson a matsayin wata gudunmowa daga gwamnatin Amurka a karkashin shirin Covax mai amar da riga kafin wannan anoba ga kasashe masu karamin karfi.

Kimanin allurai 15200 ne samfarin Johnson & Johnson aka sauke a filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai a yammacin jiya laraba wanda ke matsayin rukunin farko na tallafin da gwamnatin Amurka ta kudiri aniyar baiwa jamhuriyar Nijer domin riga kafin anobar corona .

A jawabinta, Wakiliyar hukumar OMS ko WHO Madame Blanche Anya na cewa wannan rana ta 21 ga watan yuli wani lokaci ne da aka kara samun ci gaba a yunkurin da gwamnatin Nijer ta sa gaba wajen ganin ta yiwa al’umar kasar riga kafi.

Wannan tallafi dake zuwa a wani lokacin da ake kara samun bular sabon nau’in kwayar cutar corona a wasu kasashen waje zai taimaka wa Nijer wajen karfafa matakan riga kafi inji ministan kiwon lafiyar al’uma Dr Iliassou Idi Mainassara lokacin da yake karbar wannan tallafi.

A nasa jawabin jakadan Amurka a Nijer Eric Whitaker yace dole ne a tashi tsaye domin wannan aiki na jin kai kuma wajibi ne kasashe duniya su tallafa maku a yaki da anobar corona.

A watan maris din da ya gabata ne aka kaddamar da ayyukan riga kafin corona a nan Nijer bayan isowar wani tallafin allura samfarin SINOPHARM na kasar China kafin daga bisani a karbi wasu alluarn AStrazeneca a karkashin shirin Covax sai wannan wanda kasar Amurka ta bayar samfarin Jonhson & jonhson 15200 daga cikin 300000 da gwamnatin kasar ta yi alkawalin bayarwa.

Rahoton ma’ikatar kiwon lafiyar Nijer na yammacin jiya laraba yace daga cikin mutane 5594 da suka kamu da cutar covid 19 daga farkon bular anobar a watan maris na 2020 kawo yau mutane 108 kawai ke kwance a halin yanzu wato 5292 daga cikinsu sun warke yayinda mutane 194 suka rasu sakamakon wannan masifa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Tallafawa Nijer Da Rikakafin Johnson & Johnson 15200