Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da mutuwar wasu sojojinta uku, da kuma jikkata wasu biyu bayan wani hari da aka kai musu yayin wani sintirin hadin gwiwa da suke yi da dakarun Jamhuriyar Nijar a kudu maso yammacin kasar a ranar Laraba.
Wani jami’in tsaron Amurka ya tabbatarwa da Muryar Amurka a jiya Alhamis cewa sojojin da aka kashe, dakaru ne na musamman a rundunar sojin Amurka da ake kira “Green Berets.”
Wata sanarwa da rundunar sojin Amurka a yankin Afirka ta AFRICOM ta fitar, ta tabbatar da mutuwar sojan Jamhuriyar Nijar daya.
Emmanuel Lachaussee, wanda jami’i ne a ofishin jakadancin Faransa da ke nan Washington, ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa dakarun Faransa ne suka taimaka aka kwashe sojojin Amurkan bayan wannan hari.
Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin wannan ta’asa da aka kai akan sojojin hadin gwiwar na Amurka da Nijar da yawansu ya kai goma.
Akwai akalla sojojin Amurka 800 a Nijar, wadanda ke samar da tsaro ga ofishin jakandancin kasar da kuma taimakawa wajen horar da dakarun Nijar, wadanda ke fafatawa da mayakan masu tsatsauran ra’ayin addini.