Amurka Ta Soki Wasu Jami'an Leken Asirinta

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka, Donald Trump

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta caccaki wasu jami’an hukumar leken asirinta, wadanda su ka kwarmata ma ‘yan jarida bayanai game da zargin nan na cewa Rasha na da wani tsari a Afghanistan, na biyan kudi a dau matakin soji a madadinta, wanda hakan ya jefa yunkurin tantance labarin wannan barazanar cikin rudu.

Sakatariyar Yada Labarai ta Fadar ta White House, Kayleigh McEnany, ta soki wadanda ta kira, “makiran jami’an leken asiri” saboda jefa rayukan sojojin Amurka cikin hadari, a yayin da ta kare rashin ankarar da Shugaba Trump da aka yi, game da bayanan sirrin da ba a tabbatar ba.

McEnany ta kuma yi amfani da lokacin jawabin bude taron manema labaran, wajen yin tir da jaridar New York Times, wadda ta fara yada labari game da zargin cewa, Rasha ta bai wa mayakan Taliban kudi su kashe sojojin Amurka da na gamayya a Afghanistan.

“Babu wani al’amari mai fa’ida sanadiyyar hakan,” abin da ta gaya ma ‘yan jarida kenan. Ta kara da cewa, “Wane ne kuma zai so bayar da hadin kai ga hukumar leken asirin Amurka nan gaba? Waye kuma zai so zama majiya ko mai rada ma Amurka, idan ya san daga baya za a tona mar asiri?”