Amurka Ta Yi Tayin Ladar Bayanai Kan Adnan Abu Walid al-Sahrawi

Gwamnatin Amurka ta yi tayin tukwicin miliyoyin daloli ga duk wanda ya bada bayanan da zasu taimaka a cafke mutumin da ya jagoranci harin ta’addancin da ya hallaka sojan kasar guda 4 da wasu takwarorinsu na Jamhuriyar Nijer wato shugaban reshen kungiyar IS a yankin Sahara, Adnan Abu Walid al-Sahrawi.

A yayin taron adduo’in da aka gudanar a karshen mako don tunawa da sojojin da suka kwanta dama a sanadiyyar kwantan bauna a kauyen Tongo Tongo, wanda jakadan Amurka a Nijer Eric Whitaker, ya sanar cewa, kasarsa ta fara neman Adnan Abu Walid al-Sahrawi ruwa a jallo saboda haka ta yi tanadin miliyon 5 na dala ga dukkan wanda ya tsegunta mata bayanan da za su taimaka wajen kama shugaban reshen kungiyar na IS a yankin Sahara, Abu Whalid, wanda a washegarin faruwar wannan al’amari ya sanar cewa kungiyarsa ke da alhakin kai wannan hari na ranar 4 ga watan oktoban shekarar 2017.

Da yake bayyana ra’ayinsa akan wannan kudiri Abdou Elhadji Idi na hadin gwiwar kungiyoyin FSCN na ganin abin tamkar wata hanyar karfafa wa Amurkawa gwiwa a duk inda suke a duniya, yana mai cewa hakan zai sa haka ta cimma ruwa.

Shi ma magatakardan kungiyar wanzar da zaman lafiya ta ACP Alher Alkountchi Aoutchiki, da ke daya daga cikin askarawan tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen MNJ na cewa, ba wata tantama Adnan Abu Walid al-Sahrawi na iya fadawa komar Amurkawa cikin dan kankanin lokaci muddin aka maida hankali akan tsarin samar da bayanan sirri.

To Sai dai ra’ayoyi sun sha bamban akan wannan batu domin Abdourahamane Alkassoum, wani mai sharhi akan sha’anin tsaro, na da ja a game da tasirin wannan mataki.

Ga rohoton sauti daga Wakilin muryar Amurka a yamai, Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Ta Saka Tukwicin Miliyoyin Daloli Don Cafke Adnan Abu Walid al-Sahrawi