Amurka ta Raina Karfin Kungiyar ISIS

Shugaban Amurka Barak Obama

Shugaban Amurka Barack Obama yace tun can farko Amurka ta raina karfin kungiyar ISIS wadda ta kafa Daular Islama tare da hade wasu yankunan Syria da na Iraqi.

Shugaban Amurka Barack Obama yace da farko Amurka ta raina karfin kungiyar ISIS da sauran kungiyoyin mayakan dake Syria, ta kuma zaci Iraq tana iya yakarsu.

Mr. Obama ya shaidawa shirin talabijin na CBS 60 minutes cewa,babu tabbacin cewa da an ba ‘yan tawaye masu sassaucin ra’ayi makamai tuni kamar yadda wadansu suke fada a Washington, da yanzu ana zaman lafiya a Syria.

Shugaba Obama ya dorawa tsohon Firai Ministan Iraq Nouri al-Maliki alhakin halin da Iraqi take ciki. Yace Firai Ministan ya gaza yin amfani da damar da ya samu ta hada kan kasar.

Mr. Obama yace Mr. Maliki ya rika shakkun ‘yan Sunni da Kurdawa, ya gwamnace maida hankali wajen neman goyon bayan kungiyarsa ta ‘yan Shi’a a maimakon kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Shugaban Amurkan yace tilas ne ‘yan kasar Syria da Iraqi da kuma sauran al’ummar yankin su yi tunani a kan ma’anar mutunta kowa. Yace matasan dake tunanin kan ko su ‘yan Sunni ne ko kuma ‘yan Shi’a, kamata ya yi su maida hankali kan neman ilimi da ayyuka masu kyau.