Amurka ta ki Amincewa da Wanda Iran ta Zaba Jakadanta a Majalisar Dinkin Duniya

John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Amurka ta fadawa Iran ta sake jakadanta na Majalisar Dinkin Duniya (MDD)domin ta ki amincewa da wanda kasar ta zaba kuma tana shirin turoshi majalisar.
Fadar shugaban Amurka ta White House tace ta sanarwa kasar Iran cewa ta zabi wani mutum daban domin zama jakadanta a MDD, saboda Hamid Abutalebi wanda ta zaba yanzu yana da hanu a kama Amurka 52 aka yi garkuwa da su a kasar a 1979 har na tsawon kwanaki 444, lokacinda dalibai suka kama ofishin jakadancin Amurka.

Duk da cewa Abutalebi ya zama jakadan kasarsa a Belgium da kuma a kungiyar tarayyar turai, kakakin fadar White Jay Carney, ya fadawa manema labarai cewa Hamid Abutalebi ba zai sami amincewar Amurka ba.

Rikicin garkuwa da Amurkawan wani muhimmin lokaci ne ga manyan ‘yan siyasar Farisar na yanzu, al’amari da ya kai ga yanke huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.