A jiya Litinin ne gwamantin Trump ta fito ta nuna rashin amincewar ta akan shirin kamfanin Facebook, na samar da nau’in kudin zamani na kimiyya, wanda za’a rika amfanin da su a fadin duniya.
Yayin da babban jami’in baitilmalin Amurka ya yi gargadin za’a iya amfani da su wajan yin ayyuka miyagu kamar su daukan nauyin ‘yan ta’adda da safarar mutane da kuma rashawa.
Sakataran Baitilmalin Amurka, Steve Mnuchin, ya bayyana cewa akwai matukar damuwa akan bukatar yin kudin, da babban kamfanin sada zumanta ya gabatar, da yake so ya kira kudin da suna Libra.
Mnuchin ya fada wa manema labarai a fadar White House cewa wannan hakika ya shafi harkar tsaron kasa.
Sai dai wannan kalaman nasa suna zuwa ne, bayan da shugaba Donald Trump, ya wallafa wani sakon Twitter cewa kudin Libra “bashi da inganci ko ba za’a dogara da shi ba."