A ranar Laraba Amurka ta saka takunkumin akan kamfanonin uku domin ladabtar da su, saboda ta zarge su da taimakawa Korea ta Arewa kaucewa takunkumin kasa da kasa da aka saka mata.
A jiya Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce, matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake bukatar hadin kan kasashen duniya, kan yadda za a sasanta rikicin na Korea ta Arewa.
Hukumomin Moscow sun ce takunkumin za su iya kassara tattaunawar kwance damarar makaman nukiliyan Korea ta Arewan da aka sa a gaba.
Amurka ta zargi wani kamfanin kasuwancin China da abokin huldarsa na Singapore da yin wasu takardun bogi, wadanda suka taimaka wajen saukaka safarar barasa da tabar sigari zuwa Korea ta Arewa.
A daya bangaren kuma, Sakataren Harkokin Kudin Amurka, Steven Mnuchin, ya ce Amurka a shirye take ta sake kakaba wasu sabbin takunkumin akan Turkiyya, muddin ba a saki Ba’amurken Pastor nan Andrew Brunson daga daurin talalar da aka mai ba.
A jiya Alhamis, Mnuchin ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin taron majalisar zartarwa da suka yi da shugaba Trump wanda ya samu halartar manema labarai.