Amurka Ta Kakabawa Rasha Takunkumi Mai Tsanani

Mike Pompeo Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Amurka ta tabbatar cewa Rasha ce ta saka wa tsohon ma'aikacin leken asirinta da 'yarsa guba a watan Maris a Birtaniya dalili ke nan da ta yanke shawarar ladabtar da Rasha da takunkumi mai tsananin gaske

Amurka ta sawa kasar Rasha takunkumi mai tsananin gaske bayan ta tabbatar cewa Rashan ce keda alhakin baiwa wani tsohon ma’aikacin leken asiri da ‘yarsa guba a kasar Britaniya a watan Maris.

Maaikatar harkokin wajen Amurka tace Rasha ta karya dokar kasa da kasa domin ko tayi anfani da guba akan yan kasar ta.

Wannan takunkumin wanda aka bayyana shi a jiya laraba zai fara aiki na daga ranar 22 ga wannan wata na Augusta.

Kusan dukkan abinda takunkumi zai shafa zasu hada ne da lasisin fitar da kayayyakin naurorin dake da nasaba da harkokin tsaro da ake kaiwa kasar ta Rasha, musali naurar Magana adana bayanai da ire-iren su.