Amurka Ta Kakaba Wa Wasu Jami'an Kotun ICC Takunkumi

Ranar Alhamis 11 ga watan Yuni Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya sabon takunkumin harkokin kudi da kaddarori da kuma na hana shiga Amurka akan wasu jami'an Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ake kira ICC a takaice, a wani yunkuri na hukunta su saboda binciken zargin taka doka da aka yi wa jami'an sojo da na leken asirin Amurka da ke yaki da ta'addanci a Afghanistan cikin shekaru 18 da suka gabata.

Trump ya ayyana dokar ta-baci ta kasa, yana mai kiran binciken kotun ta ICC da ke birnin Hague "barazana ga tsaron kasa da manufofin kasa-da-kasa na Amurka da ba a saba gani ba."

Umurnin na Trump ya hana jami’an kotun ICC da ba a bayyana yawansu da sunayensu ba shiga Amurka, kuma umurnin ya hana su aiwatar da harkokin kudade da kadarori a Amurka.