A yau Litinin ne wata kungiyar da Iran ke mara wa baya ta yi gargadin cewa, za ta mai da martani kan Amurka bisa hare-haren saman da ta kai wasu sansanoninta a Iraqin da Syria wadanda suka yi sanadin mutuwar mutum 25.
Wannan jan kunnen da Kataeb Hezbollah ta yi, ya biyo bayan sukar da Ministan Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran din ya yi akan harin da Amurka ta kai, wanda ya ce Amurka ta take hakkin kasar Iraki a matsayinta na kasa mai-cin gashin-kanta, kuma yin hakan aikin ta’addanci ne.
Sakataren tsaron Amurka Mark Esper, ya tabbatar da kai wadannan hare-hare a yayin da yake amsa tambayoyin manema Labarai da yammacin jiya Lahadi.
A cewarsa, jiragen yakin Amurkan sun far ma wasu sansanonin kungiyar Kataeb Hezbollah guda uku a yammacin Iraqi da wasu biyu a gabashin Syria.
Amurka ta kai wadannan hare-haren ne a matsayin maida martini bayan wani harin da aka kai kan sansanin sojan Iraqi a arewacin kasar ya rutsa da wani ma’aikacin kwantiragin ma’aikatar tsaron Amurka