Amurka Ta Kafawa Wasu Kamfanoni Takunkumi

Amurka ta kafawa wadansu kamfanoni tara, da kuma wasu mutane uku takunkumi, wadanda aka hakikanta suna da alaka da ayyukan makamai masu linzami na Koriya ta Arewa, bisa ga cewar ma’aikatar kudin Amurka.

Matakin da aka dauka jiya alhamis zai haramtawa daidaikun jama’a da kamfanoni da suka hada da kamfanonin kasar Rasha yin wata huldar kasuwanci da Amurkawan, ya kuma hanasu amfani da kaddarori da suke da su a Amurka.


An dauki wannan matakin ne yayin da Amurka take kokarin dakile ayyukan nukiliyan Koriya ta Arewa, kuma bayan gwajin makamai masu linzami biyu da kasar ta gudanar makon da ya gabata.


Wadanda aka kakabawa takunkumin jiya alhamis sun hada da kamfanonin Rasha biyu, Ardis Bearings LLC da Independent Petroleum Co, wadanda aka kafawa takunkumi sabili da samarwa Koriya ta Arewa mai da kuma kayayyakin harhada makamai masu linzami.