Wakilan majalisar dokokin Amurka 'yan Democrats da Republican, wadanda kusan dangantakar su tamkar ta kare da kenwa, sun hada karfi don aiki muhimmi, haramta yanka mage da kare a zaman abinci.
WASHINGTON DC —
Dokar wacce dan jam'iyyar Republican Vern Buchanan, daga jahar Florida da Alcee Lamar Hastings, dan Democrat suka gabatar, ta sami amincewar majalisar wakilan Amurkan a jiya Laraba.
Dokar ta ayyana tarar dala dubu biyar, akalla Naira milyan daya da dubu dari takwas, kan duk wanda aka kama yaci da saninsa, ko ya kashe, ko yayi safara, ko ya saya, ko ya sayar, ko ya bada kyautar naman kenwa ko kare a zaman abinci.
Amma dokar tayi uzuri ga wadanda suka yi a zaman wata al'ada ko sharadi na addini, kamar yadda wasu kabilun indiyawa suke yi.