Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa irin rahotanni dake fitowa daga Ghana kan yaki da cin hanci da rashawa, bayanda ya gana da shugaban kasar Ghanan John Atta Mills, a fadar White House jiya Alhamis.
Da yake magana da manema labarai bayan ganawarsu, shugaba Obama yace shugaba Mills ya nuna kudurinsa na yaki da cin hanci da rashawa da kuma tafiyarda harkokin gwanati a zahiri, wadda ya taimkawa kasar mai bin tafarkin demokuradiyya ta kasance “abar alfahari ta fuskar ci gaban tattalain arziki a Afrika".
Ba tareda la’akari da wadda ya sami nasara ko ya fadi zabe ba a zabukanda za a yi kasashemu, kudurin kasashenmu biyu na tabbatar ganin jama’a ne suka zabi wakilansu a gwamnati, wan nan shine yake karfafa kasashen namu biyu.
Da yake magana, shugaba Mills yace yana da muhaimmanci a tabbatarda zaman lafiya domi a sami ci gaba.
"Babu yadda za’a sami ci gaba ba tareda zamna lafiya ba, saboda haka yana nufin tilas muyi ayyuka da zasu tabbatar an sami zamna lafiya".
Shugaban na Ghana ya kawo wan nan ziyarar ce kwanaki bayan kasar tayi bikin cika shekaru 55 da samun ‘yancin kai.