Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a gurfanar da wasu jami'an kasar Kenya gaban kuliya

Prime Ministan Kenya Uhuru Kenyatta da Majalisar wakilai William Ruto (file photo)
Prime Ministan Kenya Uhuru Kenyatta da Majalisar wakilai William Ruto (file photo)

Kotun kasa da kasa da ake cewa ICC a takaice tayi watsi da daukaka kara da wasu ‘yan kasar Kenya guda hudu suka yi, cewa tayi watsi da caje cajen da ake yi musu.

Kotun kasa da kasa da ake cewa ICC a takaice tayi watsi da daukaka kara da wasu ‘yan kasar Kenya guda hudu suka yi, cewa tayi watsi da caje cajen da ake yi musu.

Wannan shawara ko hukunci na nufin ke nan, za’a yi wa mukadashin Prime Ministan Kenya Uhuru Kenyatta da wani dan Majalisar wakilai William Ruto da tsohon shugaban ma’aikata Francis Muthaura da kuma wani jami’in wani gidan rediyo Joshau Arap Sang shari’a bisa caje cajen aikata laifuffukan musgunawa Bani Adamu.

Ana zargin mutane hudun ne da laifin shirya tarzomar data dabaibaiye kasar Kenya bayan zaben shugaban kasa shekara da dubu biyu da bakwai da aka yi rikici akan sakamakonsa.

Alkalan kotun ICC sun bada umarnin ayi shari’ar mutane hudu a watan Janairu, to amma sai suka daukaka kara. Jiya jumaa aka yi watsi da daukaka karar da suka yi.

Tana yiwuwa wannan shawarar ko hukunci tafi shafar Kenyatta da Ruto, wadanda suka ce suna da niyar yi takarar shugaban kasa nan gaba. Kimamin mutane dubu daya dari uku ne aka kashe, fiye da mutane dubu dari uku kuma suka rasa matsuguninsu a saboda bore da rikicin kabilanci da suka biyo bayan zaben shekara ta dubu biyu da bakwai.

XS
SM
MD
LG