Amurka Ta Jefa Najeriya Cikin Jerin Sunayen Kasashen Da Suka Gaza a 'Yancin Addini

Amurka, ta sa sunan Nijeriya cikin jerin sunayen kasashen da su ka gaza ta bangaren yancin addini, wanda hakan ya share fagen yiwuwar sakawa Najeriyar takunkumi, muddun ba ta kyautata al’amuranta ba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, ya ayyana kasar ta Najeriya, wacce kawar Amurka ce, a karo na farko, a matsayin abin da ya kira, “kasa mai wani takamaiman abin damuwa” game da ‘yancin addini, kamar irin kasashen da su ka hada da China, Iran, Pakistan da kuma Saudiyya.

Pompeo bai yi karin haske ba kan musabbabin saka sunan Najeriya a wannan jerin. To amma dokar Amurka ta tanaji cewa, za a ayyana kasashe haka ne, idan su ka aikata, ko kuma su ka bari aka aikata, wasu take take masu nasaba da tauye ‘yancin addini.”

Sai dai Pompeo bai hada da Indiya ba, wacce ke da ci gaba da dangantaka da Washington, kuma hakan ya harzuka da shawarar da Kwamitin Amurka kan 'Yancin Addini na Kasa da Kasa ya hada da mutanen da ba su da addini, amma masu rinjayen Hindu kan abin da ta kira mummunan koma baya a karkashin Firayim Minista Narendra Modi.

Sauran kasashen dake cikin jerin sunayen sun hada da Eritrea da Myanmar da Koriya ta Arewa da Tajiskistan da kuma Turkmenistan.