Amurka, Birtaniya,da Faransa sun kaddamar a harin ta sama ga kasar Syria kuma sun auna wasu wurare ne na musammam da suka hada da cibiyar nazarin harkokin kimiyya da bincike , sai kuma runbun sarrafa makami mai guba, dadai sauran wasu wurare dake datasiri ga kasar a harkokin tsaro.
Sakataren harkokin tsaron Amurka James Mattis, yace makasudin wannan yunkurin shine aikewa da wani sako na musamman ga gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad, wanda ake tuhuna da kai harin makami mai guba ga farar hula a cikin satin data gabata, yace haka kuma ana fata wannan hari ya zamo jan kunne domin kada ya kara yin hakan.
Mattis yace iskan gas din nan mai guba da Assad yace tuni ya wancakalar dashi ashe karya yake yi yana nan dashi.
Sau tari wannan batun ya taso gwamnatin ta Syria sai ta musunta mallaka makami mai guba balle har tayi anfani dashi.
Janar Joseph Dunford babban hafsan hafoshin na Amurka yace safiyar yau asabar za a bada cikakken bayanin wannan harin.
Dama dai tun a jiya Jumaa ne shugaba Trump yace Amurka zata ci gaba da matsa wa Assad lamba har sai ya kawo karshen wannan mummunar tabi’ar kashe mutanen sa damakami mai guba da aka haramta masa anfani dashi
A cikin jawabin da shugaba Trump yayi a daren jiya asabar yace ba laifin kowa bane illa na Rasha da Iran, domin ko suna gani Syria na kai wannan harin makami mai guba amma suka gum.
Ita ma Prime Ministan Birtaniya Theresa May ta fada a kasar yau din nan cewa bawai katsanlandan sukayi a yaki basasa da kasar keyi ba, a’a batu na ganin an canza gwamnati, tace hari da aka kai anyi ne da niyyar ganin wannan baisa wani sabon rikici ya balle a yankin da aka kai wannan harin ba, tare da kare fararen hula.