Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta sanar a ranar Alhamis cewa, Amurka na goyon bayan samar da kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Sulhu na Majalisar ga kasashen Afirka da kuma kujera guda daya da za’a yi karba-karba a tsakanin kananan kasashe masu tasowa da ke kan Tsibirai.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke kokarin gyara alaka da kasashen Afirka, inda da dama ba su ji dadin yadda Washington ke goyon bayan yakin da Isira’ila ke yi a Gaza ba, da kuma zurfafa dangantaka da kasashen tsibirin Pacific wanda ke da muhimmanci ga dakile tasirin China a yankin.
Thomas- Greenfield ta shaida wa Kwamitin Hulda da kasashen Wajen cewa “Shekara da shekaru, kasashen nahiyar suna ta kiraye-kiraye a samar da wata majalisa mai kunshe da wakilai, wacce za ta nuna kowane yanki na duniya a yau sannan ta mai da hankali akan kalubalen da muke fuskanta a yau.”