Amurka Ta Dauki Nauyin 'Yan Gudun Hijira 'Yan Kwallon Kafa

Gwamantin Amurka ta bayyan cewa wasu matasa 'yan gudun hijira su biyar, wadanda suke da basira sosai a harkar kwallon kafa, za su shiga wani shiri da ma’aikatar harkokin wajan Amurka ta ke daukan nauyi na shirin ziyarar wasanni.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da wata muhimmiyar sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

A cikin sanarwar har da adadin kudaden da za’a kashe tsakanin 1 zuwa 19 ga watan Augusta na 2019, sannan kuma sun kara da cewa yaran da suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijirar za su samu rakiya daga wadanda suke koyar da su.