Kasar Rasha ta janye mafi yawancin jiragen saman yakinta na kai hare-hare daga Syria, sannan bas u kai wani harin sama a wannan makon bag aba daya, kamar yadda jami’an Sojin Amurka suka bayyana.
WASHINGTON DC —
A jiya Juma’a Kakakin rundunar da ke lura da ayyukan Sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya Kanar Pat Ryder ya fadawa manema labarai a cibiyar tsaro ta Pentagon cewa, in har ba’a ce dukkan jiragen ba, to kuwa sun janye mafi yawancinsu daga Syria.
Rundunar sojin Rasha dai sun taimakawa Sojin Syria a wannan makon wajen yakar ‘yan ISIS a garuruwan Palmyra da Tadmur, sai dai wannan agajin hare-haren sun bada shi ne ta hanyar amfani da sojojin da ke yaki ta kasa.
Ryder yace har yanzu Sojojin na Rasha na agazawa yakin na Syria a fakaice, sannan ta mayakan kasa ba ta amfanin da jiragen yakinsu ba.
Sannan har yanzu akwai jirginsu na dakon jiragen yaki da kuma masu saukar Ungulu a tare da Sojojin mayakan kasa.