Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pervez Musharraf tsohon shugaban Pakistan ya arce zuwa Dubai


Pervez Musharraf tsohon shugaban kasar Pakistan
Pervez Musharraf tsohon shugaban kasar Pakistan

Tsohon shugaban mulkin soja na kasar Pakistan da ake zarginsa da cin amanar kasa ya fice daga kasar

Tsohon shugaban mulkin soja na kasar Pakistan, Pervez Musharraf da ke fuskantar tuhuma kan zargin cin amanar kasa, ya fice daga Pakistan bayan da aka dagedokar haramta mai fita daga kasar.

Kotun kolin kasar ta Pakistan ce ta ba da umurnin a dage dokar a farkon wannan mako.

Tuni dai Musharraf ya tashi zuwa Dubai a yau Juma’a, inda ake sa ran zai je neman magani kan wata cuta da ya ce ya jima yana fama da ita.

Ya kuma yi alkawarin zai dawo kasar ta Pakistan domin fuskantar tuhumar da ake mai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG