Ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da kawo karshen nukiliyar Koriya Ta Arewa.
WASHINGTON D.C. —
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce takunkumin da aka kakaba ma Koriya Ta Arewa zai cigaba da aiki har zuwa karshe, wato bayan da aka yi cikakken bincike aka tabbatar cewa an kawo karshen shirye-shiryen nukiliya a kasar kamar yadda Shugaba Kim Jong Un ya yi alkawari.
Da ya ke magana yau dinnan Lahadi a wani taron manema labarai a birnin Tokyo na Japan da takwarorin aikinsa na Koriya Ta Kudu da Japan, Pompeo ya ce, "A yayin da mu ke samun karfin gwiwa sanadiyyar tattaunawar da ake yi, cigaba da tattaunawa bai isa ya sa a dage takunkumin ba."