Amurka Ta Ce Ana Samun Ci gaba a Shirye-shiryen Taronta Da Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ranar 8 ga watan Fabrarirun 2019 a farfajiyar Fadar White House

A wani sakon Twitter da ya wallafa har ila yau, shugaba Trump, ya ce yana fatan haduwa da twakaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim, inda za su ciyar da batun zaman lafiya gaba.

Wakilin Amurka na musamman kan hulda da Korea ta Arewa, Stephen Beigun, ya ce an samu ci gaba a tattaunwar da aka kammala a jiya Juma’a a Pyongyang, kan shirye-shiryen taron da za a yi a karo na biyu da Korea ta Arewan a ranakun 27 da 28 ga watan nan.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana a shafinsa na Twitter a baya cewa, wannan zama da za a yi da shugaba Kim Jong Un, zai wakana ne a Hanoi, babban birnin Vietnam.

A wani sakon Twitter da ya wallafa har ila yau, shugaba Trump, ya ce yana fatan haduwa da twakaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim, inda za su ciyar da batun zaman lafiya gaba.

A ranar 12 ga watan Yunin bara, shugabannin biyu suka hadu a kasar Singapore inda suka tattauna kan yadda Korea ta Arewa za ta kwance makamanta na nukiliya domin a dage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata.

Sai dai duk da wannan zama da aka yi, kasashen biyu sun yi ta zargin juna da kin cika alkawuran da suka dauka, inda Amurka ke zargin Korea ta Arewa da nuna jinkiri wajen ruguza makaman na nukiliyanta.