Amurka Ta Cafke Wasu Miyagun Kwayoyi a Bakin Iyakarta Da Mexico

Jami’an gwamnatin tarayyar Amurka sun kwace miyagun kwayoyi masu dimbin yawa daga hannu masu fasa kwauri dake ratsawa ta wata hanyar karkashin kasa tsakanin iyakar Amurka da Mexico su shigo kasar.

A ranar 19 ga watan Maris ne jami'an gwamnati suka gano ramin mai tsawon mitoci 600 a karkashin wasu dakunan adana kayayyaki daga iyakar arewacin Mexico, ta birnin Tijuana zuwa birnin San Diego dake kudancin jihar California a Amurka.

A cikin kwayoyin da aka gano a ramin, akwai hodar iblis da ta kai kusan kilo 600, da kilo 1,360 na tabar wiwi, sai kuma kananan kwayoyi kamar su heroin da fentanyl da sauransu. Hanyar shiga ramin na kusa da sabuwar katangar kan iyaka da shugaba Donald Trump ya kai ziyara a cikin watan Satumban bara, wadda take da muhimmanci a manufofinsa masu tsauri a kan hana bakin haure shiga Amurka.

Masu sukar lamiri sun ce katangar kan iyakar ba zata yi wani tasiri a kan yawan ramukan karkashin kasar ba, da ‘yan fasa kwaurin suka saba amfani dasu suna shiga Amurka.

A cikin watan Janairu ma an gano makamancin wannan ramin mai tsawon mitoci 1,300, mai hanyar jirgin kasa kuma akwai wutar lantarki da hanyoyin shigar iska a cikinsa. Jami’an tarayya Amurka sun ce shine rami mafi tsayi a karkashin kasa da aka gano a kan iyakar Amurka da Mexico.