Amurka ta bi sahun masu sukar juyin mulkin Mali

  • Ibrahim Garba

Dakarun kasar Mali

Amurka ta bi sahun masu yin Allah wadai da juyin mulkin da,

Amurka ta bi sahun masu yin Allah wadai da juyin mulkin da, ga alamu, wasu sojoji sun yi wa Shugaba Amadou Toumani Toure.

Wata takardar da ta fito daga Sakataren Fadar Shugaban Amurka ta White House a yau Alhamis ta yi kiran da a koma ga shugabanci na hallal a Mali ba tare da bata lokaci ba. Takardar ta ce Amurka na goyon bayan halaltacciyar zababbiyar gwamnatin Shugaba Toure.

Wani gungun soji sun yi shelar kaddamar da juyin mulki a gidan talabijin din Mali a yau Alhamis, bayan sun kame gidan yada labaran gwamnati da fadar Shugaban kasa.

Sojojin sun ce sun dau wannan matakin ne saboda gazawar Shugaban kasar wajen yaki da ‘yan awaren kabilar Azbinawan arewacin kasar.

Chairman din kwamitin gudanarwar Kungiyar Tarayyar Afirka, Jean Ping, ya bayar da wata sanarwar da a ciki yak e sukar boren da cewa sam babu hujjar yin sa.

Kungiyar Tarayyar Turai na kiran da a yi maza a koma ga gwamnati ta halal. Kuma tsohuwar mai mulkin mallakar Mali wato Faranasa ta ce ta dakatar da hulda da Mali, kuma ta ce kar a tabi lafiyar Shugaba Toure.

Ba a san inda Shugaban kasar ya ke ba, kodayake rahotannin wasu kafafen yada labarai na nuna cewa yana samun kariyar dogarawan tsaron Shugaban kasa a wani sansanin soji.