Jakadiyar Amurka a kasar Nijar yayinda take mika kayan ga mahukuntan Nijar tace kayan zasu karfafa askarawan kasar ta Nijar wajen yaki da Boko Haram.
Tace nufinsu shi ne su dakatar da Boko Haram dalilin da ya sa suke taimakawa kasashen dake fama da ta'adancin kungiyar ke nan domin a ragargaza kungiyar.
Yayinda yake magana ministan tsaro na jamhuriyar Nijar Malam Kala Muntari ya nuna mahimmancin taimakon. Yace taimakon ya zo kan lokaci domin kayan aikin zasu karawa dakarun kasar karfin gwuiwa. Ya kara da cewa taimakon ya tabbatar ma kasar Nijar Amurka na tare da su.
Wani mai nazarin harkokin tsaro a kasar ta Nijar Umaru Maisaje yana cewa taimakon da Amurka ta ba kasarsu abun godiya ne saboda wai Amurka ta ga kasar na cikin tsakan tsakani wanda yana da wuya.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5