Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ta ziyarci rumbun ajiyar magunguna na Najeriya inda aka jibge gudunmowar da kasarta ta baiwa Najeriyar, inda babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na Najeriya Dr Faisal Shu'aib ya marabceta.
Gwamnatin Amurka kawo yanzu ta baiwa Najeriya tallafin da aka kiyasta na sama da dala milyan dari da talatin a fannin alluran rigakafi gudanarwa, da sauran tsarabe tsarabe dake tattare da batun na rigakafin,
Amurkan kazalika ta kuma sa hanu wajen horas da sama da jami'an soji da fararen hula dubu dari biyu wajen shawo kan annobar cutar numfashin da kuma tsarin kandagarki dake da alaka da cutar.
Amurka ta nemi yan Najeriya dasu je a masu allurar rigafin don tsare kansu daga cutar abin da tace zai karfafa ba kawai lafiyar yan kasa kadai ba amma zai ma taka rawa a kokarin da ake na shawo kan cutar a duniya,
Kowane mutum inji Amurkan na da irin rawar da zai taka wajen wajen marawa kokarin da duniya keryi na dakile cutar ta corona, sabodahaka Amurka zataci gaba da aiki tare da ma'aikatar lafiya ta Najeriya da ma hukumar yaki da cututtuka ta kasar wajen ganin bayan cutar corona