Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) da hadin gwiwar ma'aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani ta tarayyar Najeriya zasu tattaro masu ruwa da tsaki fiye da 200, domin halartar "taron duniya akan shigar da kowa cikin harkar sadarwar zamani da amfani da kirkirarriyar basira a nahiyar Afrika.
Mahalarta taron zasu tattauna akan damammaki da kalubale dake akwai a harkar bunkasawa da yada amfani da kirkirarriyar basira
Sannan mahalarta taron zasu tantance tare da daidaita dabarun gudanar da kirkirarriyar basira a tsakanin Amurka da kasashen nahiyar Afrika domin bada dama ga basirar ta yadu.
Taron zai dabbaka a kan shirin gwamnatin Biden da Harris na samar da sauye-sauye a harkar sadarwar zamani a nahiyar Afirka, wanda zai zuba jari akan fadada fasahar sadarwar zamani da harkokin ilmi a daidai lokacin da ake karfafawa tare da samar da yanayin da zai bunkasa kasuwancin zamani a fadin Afirka.
Tawagar Amurka za ta kasance karkashin jagorancin jakadan musamman na riko akan fasahohin musamman masu mahimmanci, Dr. Set Center, da mataimakin sakataren harkokin wajen amurka akan al'amuran afrika, Joy Basu kuma za a gabatar da nadadden jawabi daga Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Kurt Campbell.