Amurka Na Tuhumar Wasu Mutane 3 Kan Badakalar Kudi Da Ta Shafi Iran

Hedkwatar Ma'aikatar Shari'ar Amurka da ke birnin Washington radar 13 ga watan Yuli, 2018.

Ma’aikatar shari'ar Amurka ta tuhumi wasu mutane 3, wadanda ake zargi da hannu a wata badakala da masu shigar da kara suka ce yunkuri ne na fitarwa da shugaban addinin Iran daloli daga Amurka. 

Ana tuhumar Muzzamil Zaidi, ba’amurke mazaunin Qom a Iran da Asim Naqvi shi ma ba’amurke mazauni Houston, da kuma wani dan kasar Pakistani Ali Chawla shi ma mazaunin Qom, da keta wata dokar kasa- da-kasa da ta shafi tattalin arziki.

A ranar Laraba ma’aikatar shari’ar ta ce, wadanda ake tuhuma suna da alaka mai karfi da dakarun juyin-juya halin kasar ta Iran.

Ma’aikatar shari’ar ta yi zargin cewa Zaidi, Chawla da wasu mambobin wata kungiya da ake kira "Islamic Pulse.

Suna kuma karbar umurni ne daga shugaban addini Ayatollah Khamenei, don karbar wasu kudaden haraji da suka shafi addini a madadinsa, don su aika da su kasar Yemen.