Mai bincike na musamman kan katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a zaben Amurka na 2016, jiya Jumma’a ya tuhumi wani kamfanin Rasha wanda ya yi shigar burtu ya na aika-aikarsa ta kafar sada zumunta, da kuma ma’aikatan kamfanin su 12 da mai samar da kudin tafi da kamfanin, a tuhuma ta farko da aka yi ma ‘yan Rasha da ake zargi da katsalandan a zaben na Amurka.
Tuhumar, wadda wani gangun masu taya alkali yanke hukunci ya yi a nan Washington DC, ta hada da zargin cewa kamfanin, mai suna Cibiyar Bincike Ta Yanar Internet, wanda ke birnin St. Petersburg, wanda kuma ke da alaka da Fadar Shugaban Rasha ta Kremlin, ya kaddamar da wani shiri na goyon bayan Shugaba Donald Trump a zaben 2016.
Masu gabatar da kara sun kuma tuhumi mai samar da kudin tafi da kamfanin, wani dan kasuwa a Rasha mai suna Yevgeny Prigozhin da wasu kamfanonin kuma biyu da ke karkashinsa.
Mataimakin Attoni-Janar din Amurka Rod Rosenstein ya ce ‘yan Rasha sun hada baki wajen yinkurin haddasa rashin jituwa a Amurka da kuma cusa shakku a zukatan mutane game da sahihancin dimokaradiyya.