Amurka Na Son A Hukumta Wadanda Suka Kashe 'Yan Shi'a A Zaria

Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky shugaban 'yan Shi'a dake da hedkwatarta a Zaria

Cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar wadda kakakinta John Kirby ya sawa hannu tace Amurka na son ganin a hukumta duk wadanda suke da hannu wajen kashe 'yan Shi'a a Zaria lokacin da suka yi taho mugama da sojoji

Ranar biyar ga wannan watan ne gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wata farar takarda akan rikicn da ya faru tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zaria cikin watan Disamban bara inda 'yan Shi'a da dama suka rasa rayukansu kana aka garkame jagoransu Shaikh Ibrahim El-Zakzaky.

Ko baicin an hukumta wadanda suke da hannu a kashe-kashen, Amurka tana son gwamnatin Najeriya ta mutunta hukumcin wata babbar kotu da ta bada umurnin a saki jagoran 'yan Shi'an da matarsa cikin kwanaki 45.

John Kairby, kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

Farfasa Dahiru Yahaya na Jami'ar Bayero na goyon bayan wannan matsayin na gwamnatin Amurka. Yace Najeriya ba zata zama kasa ta zamani ba sai tilas ta bi doka. Yace tilas mai laifi a nuna masa laifinsa. Tilas ne kuma wanda aka cuta a bashi hakkinsa. Inji shi abun da aka yi a Zaria ba'a taba yinsa ba koina a duniya a ce sojojin kasa sun ci 'yan kasa.

To saidai a baya bayan nan gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana 'yan kungiyar El-Zakzaky a matsayin 'yan ta'ada kuma ta haramtasu a jihar lamarin da Amurka tace bata ji dadin hakan ba..

A cewar babban hadimin Shaikh Ibrahim El-Zakzaky Farfasa Abdullahi Danladi su ba 'yan ta'ada ba ne. Yace masu yada wannan karya su keyi kuma sun san hakan.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Na Son A Hukumta Wadanda Suka Kashe 'Yan Shi'a A Zaria - 2' 19"