A cigaba da bayyana fushinsu kan abin da su ka kira kashe su da kuntata masu da ake yi a Najeriya, ‘yan mas’habar Shi’a sun yi zanga-zangar lumana ta kiran a daina abin da su ka kira tsananin da ake gallaza masu; sun a masu bukatar a saki Shugabansu na kasa baki daya Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky, wanda su ka koka cewa bayan kashe masa ‘ya’ya babu gaira babu dalili sai aka kuma cigaba da tsare shi.
‘Yan Shi’an sun koka kan kashi masu ‘yan uwa da dama da kuma jagororinsu. Su ka ce akan saba ma dokokin Najeriya wajen nuna masu tsanai don kawai nuna fin karfi. Dya daga cikin shugabannin ‘yan Shi’a din mai suna Daud Zakariya ya ce an mai da su saniyar ware a Najeriya inda ake ta kashe su tun daga 2014 aka shiga tsananta kashe su har da ‘ya’yan na Zakzaky ba tare da hukuma ta dau matakin ladabta wadanda su ka yi kasan ba. Ya ce a 2015 an hallaka masu mutane sama da dubu daya; ya ce a 2016 ma an hallaka masu mutane a Funtuwa da wasu wurare. Malam Zakariya y ace a makon jiya ma an kashe masu mutane wajen 100 a Kano.
Da ya ke tofa bakinsa kan kashe-kashen da ke faruwa, Dr. Aliyu Tilde y ace bai kama a kashe mutane ko kuma a bar mutanen gari na kashe su don kawai ba a basu takardar izinin yin taro ba. Y ace ya kamata a yi hattara game da yadda ake ta aikata kashekashen. Y ace ya kamata a koyi darasi daga yadda kungiyar Boko Haram ta bullo.