Amurka Na Shirin Tura Karin Dakaru 200 Zuwa Syria

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter l

Sakataren tsaron Amurka, Ash Carter ya ce Amurka na tura karin dakarun 200 zuwa Syria.

A yau Asabar Carter ya ce za a yi amfani da dakarun ne wajen fatattakar ‘yan kungiyar IS daga Raqqa, birnin da kungiyar ke ikrari a matsayin hedkwatarta.

Ya ce dakarun za su marawa sauran sojojin Amurka na musamman su 300 da ke girke a kasar ta Syria, wadanda sun kware a fannin horarwa da kuma kwance bama-bamai.

Sakataren tsaron na Amurka ya yi wadannan kalaman ne yayin wani taro da aka yi a Bahrain kan tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Carter ya ce Rasha wacce ita ce babbar kawar gwamnatin shugaba Bashar al- Assad, ta taimaka ne kawai wajen sake tsunduma kasar cikin halin kakani-kayi.