A lokacin da ya kawo ziyara nan Amurka Fira ministan India Nerendra Modi ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House inda suka yi alkawarin karfafa dangantakar yarjeniyoyi tsakaninsu kamar Amurka da kawayenta na kud-da-kud.
WASHINGTON D.C. —
Shugaban Amurka Donald Trump da Fira ministan India Narendra Modi sun yi alkawarin aiki tare wajen karfafa yarjajjeniyoyin tsaro da na tattalin arziki dake tsakaninsu.
Kasashen biyu na hankoron hada kai wajen abin da ya shafi na'urorin tsaro masu inganci irin yadda Amurka kan yi da kawayenta na kud-da-kud, a cewar wani bayanin Fadar White House da aka fitar da yammacin jiya Litini.
Firaministan na India, wanda ya bayyana tattaunawarsa da Shugaba Trump da cewa ta yi tasiri, ya baiwa Trump wata kyauta ta karramawa a wurin shakatawa na Rose Garden bayan kammala tattaunawar ta su.