Yayin da kasar China ke cigaba da tilasta tsiraru da wasu rukunin al'ummarta ayyukan da su ka wuce kima don amfanarta, gwamnatin Shugaban Amurka Donald Ttrump na shirin haramta sayen kayan da China ta sarrafa da gumin wasu al'ummominta.
WASHINGTON DC —
Jaridar New York Times ta bayyana cewa gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na kokarin kakaba takunkumi kan dukkanin abubuwan da aka sarrafa da audugar yankin Xinjiang na kasar China, a dai dai lokacin da ake samun rahotanni masu zargin cewa ana tilasta wa mutane yin ayyukan da suka keta hakkin dan adam a yankin Xinjiang na China.
Jaridar ta ce, mutum uku wadanda suke da masaniya kan lamarin ne suka bayyana hakan kuma za a fara aiwatar da wannan takunkumin ne a yau.
Dama dai a baya an sha samun rahotanni masu nuna yadda mutane a Xinjiang, musamman ma al'ummar Musulmin Uighur ke fuskantar muzgunawa da kuma yadda ake sa su ayyukan da basu dace ba.