WASHINGTON D.C. —
Kusan membobi da shugabannin kungiyar tsageran MS-13 guda ashirin da hudu ne aka kama ake kuma tuhuma, a zaman wani bangaren shirin jami’an tsaron gwamnatin tarayyar Amurka na wargaza shugabancin kungiyar.
Shugaba Donald Trump, wanda ya sha alwashin murkushe kungiyar ne ya sanarwar da lamarin a ranar Laraba a Fadar White House, tare da Atoni Janar William Barr, da wasu manyan jami'an tsaron kasar a gefensa.
"Mun kaddamar da wani samame na tarihi, wanda ya kai ga kame da kuma tuhumar membobin kungiyar MS-13 da shugabanninsu da yawa a fadin Amurka," in ji Trump.
Trump ya ce cikin kamen da aka yi har da manyan membobin kungiyar MS-13 “a matakin kololi” kuma a cikin ‘yan kwanakin nan aka yi samamen a fadin kasar.