Amurka Na Kokarin Fitar Da Manhajan China Daga Yanar Gizon Amurka

Gwamnatin Shugaba Trump ta fada a yau Laraba cewa, tana nan tana kokarin fitar da manhajar yanar gizo ta China da ba’a amince da ita ba, daga tsarin yanar gizo na Amurka, kana ta bayyana manhajar aikewa da sakwannin bidiyo ta TikTok mallakar China, da manhajar aikewa da rubutattun sakwanni ta WeChat, a zaman “manyan barazana.”

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce shirin da Amurka ke fadadawa da ta kira “tsabtace yanar gizo”, zai mai da hankali akan Abubuwa biyar, da suka hada da matakan hana manhajoji da dama na China, da kuma kamfanonin sadarwa na China daga mallakar muhimman bayanai na ‘yan kasar Amurka da ‘yan kasuwarta.

Sanarwar ta Pompeo ta zo ne bayan shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar haramta TikTok. Manhajar ta aikewa da sakwannin bidiyo mai dimbin jama’a tana fuskantar kakkausan suka daga ‘yan majalisar dokoki da gwamnatin Amurka, akan damuwar kalu-balen tsaron kasa, a yayin da tankiya ke kara zafafa tsakanin Washington da Beijin.


Yanzu haka TikTok na fuskantar wa’adin nan da ranar 15 ga watan Satumba, da ko dai ya sayar da ayukansa na Amurka ga kamfanin Microsoft, ko kuma a haramta shi nan take.

Pompeo ya kuma ce Amurka na kokarin hana kamfanin sadarwa na Huawei na kasar China, daga dasa na’urori, ko kuma saka manhajarsa domin saukewa da dorawa wayoyin salula na Amurka.