Amurka Na Katsalandan Ga Harkokin Cikin Gida Na Iran - Inji Rasha

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, ta yabawa masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Iran a wani taron gaggawa da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar, yayin da kasar Rasha ke sukar Amurka kan abin da ta kira katsalandan ga harkokin cikin gida na Iran.

Jiya Juma’a ne Amurka ta kira taron gaggawa domin tattauna zanga-zangar dake faruwa a Iran, wadda mutane 22 suka rasa rayukansu, ta kuma yi sanadiyar kama mutane sama da dubu ‘daya.

Tun makon ya gabata aka fara zanga-zanga a manyan biranan Iran, na adawa da kuma goyon bayan gwamnati.

Haley ta yi kira ga gwamnatin Iran da ta dakatar da rufe bakin mutanenta, ta kuma mayar musu da yanar gizon da aka katse.

Ta kuma ce yakamata al’ummar duniya su ‘kara azama wajen goyon bayan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Amma masu sukar Amurka a batun, ciki har da Rasha da kuma ita kanta Iran, sun ce babu ruwan al’ummar duniya game da zanga-zangar dake faruwa a Iran.