Shugaba Trump ya kuma umurci majalisar tsaron kasar ta yi dubi kan ko janye takunkumin da aka sakawa Iran ya na da muhimmanci ga tsaron Amurka.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson ne ya bayyana hakan a wata wasika a jiya Talata, wacce aka aike wa kakakin majalisar wakilan, Paul Ryan.
Tillerson ya ce ya zuwa jiya Talata, Iran na bin ka’idojin da aka gindaya mata a karkashin yajejeniyar da aka kulla da ita a shekarar 2015 tsakaninta da Amurka da Birtaniya da Faransa da China da Rasha da kuma Jamus.
A wani mataki na neman a janye mata takunkumin da aka kakabata sanadiyar shirin nata na mallakar makamashin nukiliya, Iran ta amince ta dauki wasu matakai, ciki har da cewa ba za ta hada ko kuma ta mallaki makaman na nukiliya ba.
Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashe ciki har da Amurka sun kakabawa Iran takunkumin tattalin arziki, a wani mataki na neman ta yi watsi da shirin mallakar makamin nukiliyanta.