Amurka Na Cigaba Da Bankado Satar Fasahohinta Da China Ke Yi

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka Donald Trump

Kasar Amurka, ta Ma’aikatar Shari’arta, ta na cigaba da aikin bankado satar fasaharta da kuma leken asirin tattalin arziki da China ke ma ta, duk kuwa da cewa annobar corona ta janyo rufe akasarin bangaren shari’ar kasar.

Cikin ‘yan kwanakin nan, Ma’aiktar ta Shari’a ta daidaita da tsohon furfesan jami’a da ke Atlanta sannan ta tuhumi wasu mutane biyu da wani shiri na farauta ma kasar China masu hazaka da za su mata aiki.

Wadannan tuhume-tuhumen na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar Bincike Ta FBI da kuma Hukumar Tsaron Na Cikin Gida su ka yi gargadi wannan makon cewa wasu masu kutsen intanet masu alaka da gwamnatin China na kokarin satar binciken da Amurka ke yi game da cutar corona, da magunguna da kuma hanyoyin jinya.

A yayin da annobar corona ta durkusar da kotunan gwamnatin tarayya tare tilasta akasarin ma’aikatan gwamnatin tarayyar aiki a gida, jami’an tsaro sun ce ta yiwu ma a bayyana sakamakon aikin dakile sace-sacen ayyukan fasaha da China ke yi, da sauran binciken da ake yi, da dai sauransu.